A cikin "Sanarwar Camp David" da kungiyar ta fitar bayan da aka kawo karshen taron koli na kungiyar a ranar 19 ga wata, an nuna cewa, ko da yake an fara samun kyakkyawar alamar farfado da tattalin arzikin kasa da kasa, amma har yanzu ana fuskantar kalubale mai tsanani, saboda haka, an yi maraba da tattaunawar da kasashen Turai suke yi game da yadda za a daidaita manufofin kasafin kudi lokacin da ake kokarin bunkasa tattalin arziki.
Wannan sanarwa ta jaddada cewa, ya kamata kasashen duniya su dauki amintattun matakan farfado da kuma bunkasa tattalin arziki wadanda za su taka rawa wajen kara saurin bunkasa tattalin arziki da biyan bukatun da ake da su ba tare da wata tangarda ba. Amma tabbas ne wadannan matakan tattalin arziki da ya kamata kasashe daban daban su dauka za su sha bamban. (Sanusi Chen)