Wannan taro na kwanaki 2 ya hada a wuri guda shugabannin kasashen Britaniya, Faransa, Jamus, Italiya, Japan, Rasha da kuma kasar Amurika. Taron zai tattauna kan maganar matsalar tattalin arziki a kasashe masu amfani da kudin EURO, maganar nukiliyar kasar Iran, rikicin kasar Siriya da kuma maganar makamashi da ta kalaci a duniya da dai sauransu.
Duk da ajandar taron ta kunshi abubuwa da dama, masu nazari kan yadda lamura ke gudana sun furta cewa, taron ba zai fito da wani muhimmin sakamako ba.
Har ila yau, kafin an fara taron a ranar Jumma'ar, shugaban kasar Amurika Barack Obama ya gabatar da wani shiri na samar da abinci ga nahiyar Afrika. A game da wannan tsari na samar da kalaci ga nahiyar Afrika, kudi biliyan 3 na dalar Amurika ne, ake fatan sassa masu zaman kansu su kawo, domin samar da kalaci da kuma gudanar da ayyukan noma a Afrika, a yayin da ake kira ga kasashe masu karfin tattalin arziki na kungiyar su kawo tasu gudunmowar ta daban.
Obama ya sanar da cewa, kasashen kungiyar G8 na da babban nauyi da ya rataya a yuwansu, sabili da haka yana da muhimmanci su tashi tsaye wajen yakar yunwa da tamowa a Afrika , duk da babban kalubalen da kasashen ke fuskanta, ciki har da samar da aikin yi, daidaita yanayin da ake ciki a kasashe masu anfani da kudin EURO, da kuma farfado da tattalin arzikin duniya
Sabon tsarin da aka kirkiro, mai sunan sabon hadadden fasali domin gwagwarmaya da yunwa da samar da abinci, na da burin kara jawo kudin jari daga masu zaman kansu da bunkasa sabbin fasahohi ta bangaren noma.
Obama ya sanar da cewa, kamfanoni 45 da suka hada da manyan kanfanoni na kasa da kasa da na Afrika sun taimaka da kudi biliyon 3 na dalar Amurika domin bunkasa ayyukan noma da samar da abinci a Afrika.(Abdou Halilou).