Tun ranar 1 ga watan Janairu na shekarar bana, kasar Burtaniya ta karbi shugabancin kungiyar ta G8 na wannan karo. Cikin wasikunsa, David Cameron ya nuna cewa, a nashi wa'adin aikin, zai mai da hankali kan ayyukan bunkasa tattakin arziki da kuma kara guraban aikin yi, bugu da kari, kasar Burtaniya za ta goyi bayan cinikayya mara shinge, hukunta masu gudun haraji, inganta tsarin gudanar da ayyukan gwamnati a fili, ta yadda za ta iya kafa wani tsarin tattalin arziki da na gwamnati da na zamantakewar al'umma , inda za a yi kome a bayyane domin jama'a su gani.
Bugu da kari, yayin da ake maganar taron kolin G8 da za a yi a yankin Arewacin Ireland ta kasar Burtaniya a watan Yuni mai zuwa, David Cameron ya bayyana cewa, zai mai da hankali kan harkokin da suka shafi cinikayya, haraji, da kuma gudanar da harkokin gwamnati a fili, don haka ya yi kira ga shugabannin G8 da su inganta ayyukan tattalin arziki cikin 'yanci, da gudanar da ayyukan gwamnati a fili da kuma bai wa kamfanonin kasar goyon baya ta yadda za a iya cimma burin bunkasa tattalin arziki. (Maryam)