Kungiyar G8 za ta fitar da shirin samar da kudin taimako dala biliyan 40 ga kasashen Larabawa
Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka shirya bayan kammala taron koli na kungiyar G8 a ran 27 ga wata, cewar kungiyar za ta fitar da wani shirin samar da kudin taimako dala biliyan 40 ga kasashen Larabawa da ke cikin halin rudani ta yadda za su farfado da tattalin arzikinsu da kuma samun ci gaban zaman al'ummarsu.
Haka kuma shugaba Sarkozy ya ce, a cikin wannan shirin da ya kunshi dala biliyan 40, dala biliyan 20 zai fito ne daga hukumomin kudi na kasa da kasa ban da asusun ba da lamuni na duniya wato IMF. Kuma za a samar da kudi dala biliyan 10 bisa yarjejeniyar da bangarorin biyu suka daddale, kasashen da ke yankin Gulf kuma za su samar da saura dala biliyan 10 na adadin kudin.(Kande Gao)