An bude wani taron yaki da ta'addanci ranar Alhamis don tattaunawa kan hadin kan shiyyoyi, da ma duniya baki daya kan dabarun yaki da ta'addanci.
Ofishin aiwatar da matakan yaki da ta'addanci na MDD (CTITF), tare da gwamnatin kasar Switzerland ne suka dau nauyin gabatar da shirin wanda ya samu zuwan wakilan gwamnatoci sama da 200, masana kan yaki da ta'addanci na kasashe, wakilai daga MDD da sauran kungiyoyi masu wannan harka a kasa da kasa, na shiyyoyi da makamantansu.
Shugaban na CTITF kuma sakatare janar na MDD a fuskar harkokin siyasa Jeffrey Feltman cikin jawabinsa na bude taron ya ce, wannan taro ya zo a cikin yanayi da al'ummar duniya ke fama da ta'addanci da tsatsauran ra'ayi.
Feltman ya ci gaba da cewa, ta yaya ne za'a tabbatar da cewa, ba'a shigo da batun kare hakkin bil-adama ba a yayin yaki da ta'addanci.
Wannan taro dai na fatan mai da hankali kan batutuwa kamar yin aiki da matakai da aka tsayar wajen yaki da ta'addanci a duniya, cikin hadin gwiwa a shiyyoyi, da kuma yadda za'a samu ci gaba daga yaki da wannan mummunan aiki zuwa magance abin da ke haifar da shi. (Lami)