Babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya taya al'ummar kasar Kenya murnar kammala babban zabe kasar cikin kwanciyar hankali da lumana, yana mai cewa, al'ummar kasar ta Kenya sun cancanci jagoranci na gari.
Wata sanarwa da ofishin Sakataren MDD ya fitar, ta kara da jinjinawa al'ummar kasar, saboda irin hakuri da juriya da suka nuna, yayin da suke dakon sakamakon zaben.
A ranar Jumma'ar da ta gabata ma sai da Ban Ki-Moon ya tattauna da manyan 'yan takarar shugabancin kasar ta Kenya Uhuru Kenyatta, da Rella Odinga ta wayar tarho, inda ya sake bukatar su da su furta kalamai da zasu kwantar da hankulan magoya bayansu, yana mai tuna musu alkawarin da suka dauka, na warware takaddamar daka iya biyo bayan sakamakon zaben ta hanyar da doka ta tanada.
A jiya Asabar ne dai hukumar zaben kasar ta Kenya, ya bayyana sunan Uhuru Kenyatta, a matsayin wanda ya lashe zaben da aka kada, da kuri'u da yawansu yakai miliyan 6.17, yayin da kuma Raila Odinga, ke biye masa a yawan kuri'un zaben, na ranar Litinin 4 ga watan nan da muke ciki. (Saminu)