Don gane da haka, gamayyar kasa da kasa sun yi suka mai tsanani ga kasar Koriya ta Arewa.
Yayin da yake ganawa da babban sakataren MDD Ban Ki Moon ran 11 ga wata, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bayyana cewa, kamata ya yi kasar Koriya ta Arewa ta daina yin tsokanar tashin hankali, kuma ya jadadda cewa, Amurka za ta dauki matakai yadda ya kamata wajen kiyaye yanayin tsaron kasar da na wasu kasashen kawayenta.
Yayin taron manema labarai a wannan rana, Mr. Ban Ki Moon ya nuna cewa, yanayin makurdadar Koriya ya janyo hankalinsa sosai, kuma ya bukaci kasar Koriya ta Arewa da ta daina yin tsokana na tayar da hankali.
Bugu da kari, shugabar kasar Koriya ta Kudu Park Geun-hye ta bayyana ran 11 ga wata cewa, za ta yi shawarwari tare da kasar Koriya ta Arewa, ta kuma yi alkawarin cewa kasarta za ta samar da taimakon jin kai ga Koriya ta Arewa.
Bisa labarin da aka samu, ministan harkokin wajen kasar Amurka John Kerry zai isa kasar Koriya ta Kudu ran 12 ga wata da yamma, don fara ziyarar aiki a kasashen Koriya ta Kudu, Sin da kuma Japan, Kuma zai yi tattaunawa tare da takwaran aikinsa na kasar Koriya ta kudu kan harkokin yanayin makurdadar Koriya.
Haka zalika, an gudanar da taron shawarwarin ministocin harkokin wajen kasashen G8 ran 11 ga wata a birnin London. Bayan taron, ministocin sun ba da sanarwar hadin gwiwa inda suka yi suka mai tsanani kan baranazar makaman nukiliya da Koriya ta Arewa take yi, da kuma shirin kasar game da harba makamai masu linzami. (Maryam)