Kwamitin samar da zaman lafiya na Koriya ta arewa ya fada cikin wata sanarwa cewa, kasar tana da 'yancin gudanar da atisayen da kasashen Amurka da Koriya ta kudu suka yi Allah-wadai da shi.
Wannan shi ne karo na farko da Pyongyang ta mayar da martani ga harba makamai masu linzamin da ake zarginta da aikatawa, inda ta zargi Washington da Seoul da gudanar da atisayen soja cikin hadin gwiwa da na'urorin harba bama-bamai.
Ofishin shugaban kasar Koriya ta kudu ya bukaci Koriya ta arewa da ta dakatar da tsananta halin da ake ciki a zirin Koriya, bayan da Pyongyang ta harba makamai masu linzami masu cikin gajeren zango a yankin ruwanta a ranar Asabar. (Ibrahim)