Kamata ya yi bangarori daban daban su magance tsanantar da halin yankin Koriya, a cewar kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei ya bayyana a gun taron manema labaru a ranar 11 ga wata cewa, kasar Sin na kira ga bangarori daban daban da batun yankin Koriya ya shafa da su bi bukatun kasa da kasa da magance daukar matakan tsanantar da halin da ake ciki a yankin.
Mr Hong Lei ya ce, ya kamata a yi kokarin sake bude shawarwari a tsakanin bangarori shida da kara yin mu'amala da juna don sa kaimi ga cimma burin hana amfani da makaman nukiliya a yankin Koriya da kuma samun zaman lafiya a yankin har ma a yankin arewa maso gabashin nahiyar Asiya. (Zainab)