Bisa labarin da aka bayar, an ce, a ran 8 ga wata, kasar Koriya ta arewa ta sanar da rufe yankin masana'antu na Kaesong, sannan a yau 9 ga wata, ta ba da shawara ga hukumomi da masana'antu na kasashen waje da baki masu yawon bude ido a kasar da su tsara shirin janye jiki daga kasar. Game da wannan lamari, Hong Lei ya ce, bangaren Sin na adawa da dukkan matakan da za su tsananta halin da ake ciki, kuma ya nuna ki amincewa da dukkan matakan da za su kawo illa ga halin kwanciyar hankali da ake ciki a yankin Koriya.
Sannan, ya sake yin kira ga bangarorin da abin ya shafa da su yi kokari wajen tabbatar da zaman lafiya da fitar da yanki daga mawuyacin hali. (Sanusi Chen)