in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu tada kayar baya a Najeriya sun karyata barazanar kai munanan hare-hare
2013-01-30 11:19:10 cri

Babbar kungiyar nan mai tada kayar baya a yankin Niger Delta mai arzikin mai da ke Najeriya (MEND) ta karyata barazanar kai munanan hare-hare a kasar da ke yammacin Afirka sakamakon yankewa daya daga cikin mambobinta hukunci da aka yi a kasar Afirka ta Kudu.

A karshen mako ne ake zargin wani jigo a kungiyar Comrade Azizi ya bayar da wata sanarwa, cewa, 'ya'yan kungiyar ta MEND suna shirin kaddamar da jerin hare-hare don nuna rashin jin dadinsu kan hukuncin da aka yankewa Henry Okah, daya daga cikin mambobinta a kasar Afirka ta Kudu, dangane da harin bam din da aka kai ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 2010 a Abuja, babban birnin Najeriya.

Ana alakanta kungiyar ta MEND da kai hare-hare kan cibiyoyin mai na kasa da kasa da sace 'yan kasashen waje a yankin Niger Delta.

Wata sanarwa mai dauke da sanya hannun shugaban kungiyar Jomo Gbomo da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu a ranar Talata, kungiyar ta tsame kanta daga wannan rahoto kana ta shawarci hukumomi da suyi watsi da wannan bazarana ko farfaganda da nufin haifar da rashin hadin kai a kasar.

Bugu da kari sanarwar ta ce, kungiyar ba ta taba daukar Okah a matsayin shugabanta ba, face mai goyon bayan manufofinta. Don haka babu wata hujjar da za ta sa 'yan tawayen na Niger Delta su shirya wani gangami ko kaiwa wani hari domin an yanke masa hukunci.

A baya dai kafin shirin yin ahuwa na marigayi shugaba 'Yar adua ga masu dauke da makami a shekara ta 2009, kungiyar ta MEND ta dauki alhakin wasu hare-hare da aka kai, yin garkuwa da mutane da mambobinta suka yi, zagon kasa, sace-sace da lakata kayayyaki, da kuma yakin sunkuru..(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China