in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da 'yan gudun hijiran Syria 444,000 ne ke Lebanon, a cewar MDD
2013-04-29 16:48:49 cri

A rahotonta na mako-mako da ta fitar a ranar Lahadi 28 ga wata, babbar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta bayyana cewa, yawan 'yan gudun hijirar kasar Syria da suka kauracewa fadan da ake a kasar zuwa Lebanon ya tasam ma sama da 444,000.

Rahoton ya ce adadin 'yan gudun hijirar da aka yi wa rijista ya kai 330,000, yayin da sama da 113,000 ke jiran a kammala yin musu rijista.

Rahoton ya kara da cewa, a halin yanzu akwai 'yan gudun hijirar kasar ta Syria 137,000 da ke arewacin kasar Lebanon,119,000 daga cikinsu na yankin Bekaa,45,000 na tsaunin Lebanon da Beirut, kana 28,000 na zaune a kudancin Lebanon.

Kasar ta Lebanon dai na fama da matsalar tsaunuka wajen kula da yawan 'yan gudun hijirar da ke barin Syria sakamakon rikicin da ake fama da shi a kasar.

Babbar kwamishinar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD Antonin Guterres ta ce, yawan 'yan gudun hijirar Syria da ke Lebanon ya kai kashi 10 na yawan al'ummar Lebanon, kuma hakan na haifarwa gwamnati da al'ummar Lebanon babbar matsala.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China