Shen Danyang ya jaddada cewa, ma'aikatar kula da harkokin kasuwanci ta Sin ta dora muhimmanci sosai game da wannan batu, kuma ta yi hadin gwiwa da ma'aikatar kula da harkokin wajen kasar Sin da ofishin jakadancin Sin da ke kasar Ghana don yin tuntubawa da shawarwari cikin aminci tare da kasar Ghana. Shen Danyang ya ja kunne sauran Sinawa dake aiki a kasashen waje, su bi hanyar ya kamata wajen yin aiki a kasashen waje, da shiga cikin kasar, da yin aiki da samun iznin zama bisa ka'ida, don magance ayyukan da za su lahanta hakkin Sinawa da tsaronsu.
Kwanan baya ne dai, hukumomin shari'a na kasar Ghana sun cafke Sinawa sama da 100 da aka tuhume su da haka zinariya ba bisa ka'ida ba.(Bako)