A yau Litinin 13 ga wata a nan birnin Beijing fadar gwamnati, Kasar Sin ta bakin kakakinta Hong Lei ta yi Allah wadai da fashewar bam din da ya auku a cikin wassu motoci har biyu a kasar Turkiyya wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 46 tare da jikkata wassu kusan 100 a wani gari dake kan iyaka da kasar Siriya a ranar Asabar din data gabata.
Hong Lei yace Kasar Sin tayi Allah wadai da babbar murya a kan wannan mummunan hari, kuma tana mika ta'aziyyarta ga iyalan wadanda wannan hari ya shafa, da gwamnati da kuma al'ummar kasar Turkiya baki daya, sannan ta yi fatan samun sauki cikin sauri ga wadanda suka samu rauni sakamakon wannan al'amari.
A ranar Asabar ce dai motoci biyu dauke da bama bamai suka tarwatse tare da girgiza garin Reyhanli kusa da kan iyakar kasar Turkiya da kasar Siriya, wanda hakan ya jawo wani tsoro ga mazauna wurin na cewa, tashin hankalin dake faruwa a cikin kasar Siriya ya fara bazuwa a makwabtanta.
Rahotanni sun ce, an kame 'yan asalin kasar Turkiya su 9 da zargin sa hannunsu a cikin wannan harin, sannan kuma ana nan ana cigaba da bincike.(Fatimah Jibril)