in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya yi kira da a tsai da ciakken tsarin magance rikicin dake aukuwa a yankin Saleh
2012-12-11 11:11:43 cri
Wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Li Baodong, ya ba da jawabi a birnin New York hedkwatar MDD a ran 10 ga wata, inda ya jaddada wajibcin tsai da wani cikakken tsari domin tinkarar kalubalolin da ake fuskanta a yankin Sahel dake kudancin saharar Afirka, tare da mai da hankali kan batun talauci da koma baya da sauransu da ake fuskanta a yankin, bisa la'akari da ikon kasashe da kungiyoyin dake wannan yanki.

Yayin taron ministocin da kwamitin sulhu na MDD ya yi a wannan rana kan batun yankin Sahel, Li Baodong ya ce, ya kamata, a warware wasu manyan matsaloli a wannan yanki domin tabbatar da zaman lafiya da karko a yankin. Ya zuwa yanzu, ana fuskantar hali mai tsanani a wannan yanki, ciki har da talauci da koma baya wadanda suka zamo matsaloli da suka fi kawo cikas. Kasashen duniya, musamman ma kasashe masu ba da tallafi da hukumomin hada-hadar kudi na duniya, ya kamata su kara ba da taimako da tallafi, musamman ma a fannin tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma a wannan yanki.

Bugu da kari, Li Baodong ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin na mai da hankali kwarai kan halin da ake ciki a wannan yanki, kuma tana kokarin sa kaimi ga tabbatar da zaman karko da bunkasuwar wannan yanki ta hanyoyi daban-daban, tare kuma da ba da taimako gwagwadon karfinta. Koda ma a shekarar da ta gabata, Sin ta samar da tallafin hatsi sau da dama ga wasu kasashe dake wannan yanki, ban da haka, Sin na kara hadin gwiwa da kungiyar AU, da ma wasu kasashe dake wannan yanki domin dakile ta'addanci. Sin na fatan kara taka rawar da ta dace, wajen tinkarar kalubalolin da yankin na Sahel ke fuskanta tun da wuri kuma daga duk fannoni. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China