in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane kimanin miliyan 18 za su yi fama da yauwa a bana a yankin Sahel, in ji jami'in MDD
2012-05-30 10:59:04 cri

Ranar Talata 29 ga wata a birnin Geneva, mai daidaita batun jin kai a yankin Sahel na MDD Gresley ya ce, a cikin wannan shekara yawan mutanen da za su yi fama da yauwa a yankin zai haura miliyan 18, daga cikin su kananan yara kimanin miliyan 1 za su yi fama da tamowa mai tsanani.

Gresley ya yi gargadi cewa, idan ba a dauki matakai yadda ya kamata ba, yawan kananan yara da za su mutu zai kai kashi 60 cikin dari. Ban da wannan kuma, kananan yara miliyan 2 za su yi fama da matsakaicin tamowa. Ya ce, wannan zai kasance karo na uku da za a fuskanci matsalar karancin abinci a wannan yanki tun daga shekarar 2005, matsalar dake tafe za ta mai zuwa zai kawo babbar illa saboda ba al'amura ba su farfado ba tukuna yadda ya kamata.

Gresley ya ce,za a samu sauki idan aka warware matsalar karancin abinci kadai, amma a wannan yanki, ana fuskantar batun 'yan gudun hijira, abin da ya kawo wahalhalu da dama wajen farfado da yankin Sahel.

Dadin dadawa, Gresley ya ce, MDD na kokarin tattara kudi, har ila yau, yawan kudin da aka samu ya kai dala miliyan 700. Amma, an yi kiyasin cewa, yawan kudin da ake bukata domin warware wasu batutuwa ciki har da rikicin Mali ya kai dala biliyan 1.5.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China