Ban Ki-moon ya nuna cewa, MDD za ta nada wani manzon musamman domin sa ido kan aikin samar da taimako ga yankin wajen fama da matsaloli kamar su talauci, tashin hankali, sauyin yanayi da kuma bala'in halitta.
Yankin Sahel wani ziri ne tsakanin hamadar Sahara ta arewancin nahiyar Afirka da makiyayun kasar Sudan ta tsakiyar Afirka, inda yawan ruwan sama kan kai milimita kimanin 200 zuwa 600, daga arewacin yankin zuwa kuduncinsa a ko wace shekara. An yi hasashe cewa, ya zuwa karshen shekara ta 2012, yawan mutanen da za su fama da karancin abinci a yankin zai iya kaiwa miliyan 18, ciki har da yara miliyan 1 da za su fama da yunwa mai tsanani.(Maryam)