in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jamhuriyar Afirka ta Kudu
2013-03-26 10:59:13 cri
Jamhuriyar Afirka ta Kudu tana iyakar kudancin nahiyar Afirka, tare da fadin muraba'in kilomita miliyan 1.22, kuma kasar da ta kasance hade da manyan birane uku a duniya, na farko, babban birnin kasa na siyasa, Pretoria, na biyu, babban birnin kasa na majalisa, Cape Town, sannan da babban birnin kasa na dokoki, Bloemfontein.

Kasar Sin da kasar Afirka ta Kudu sun kafa dangantakar diflomasiya a ranar 1 ga watan Janairu, shekarar 1998, daga baya, dangantakar kasashen biyu ta ci gaba da bunkasuwa cikin sauri a fannoni daban daban. Sun kafa dangantakar abokantaka a shekarar 2000, sannan a shekarar 2004, kasashen biyu suka kara tabbatar da dangantakar abokantaka daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare don cimma moriyar juna bisa ka'idar nuna adalci da kuma neman bunkasuwa cikin hadin gwiwa. Bugu da kari, a watan Agusta na shekarar 2010, shugabannin kasashen biyu sun bunkasa dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi daga dukkan fannoni. Ya zuwa halin yanzu, kasar Afirka ta Kudu ta kasance abokiyar cinikayyar Sin mafi girma a nahiyar Afirka, yayin da kasar Sin ita ma ta kasance muhimmiyar abokiyar cinikayyar Afirka ta kudu. A shekarar 2012, yawan cinikayya tsakanin kasashen biyu ya kai dalar Amurka biliyan 59.9, adadin ya karu da kashi 31.8 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekarar 2011. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China