Kasar Sin za ta kiyaye tsaron lafiya da halaltattun hakkokin Sinawan da ke kasar Ghana
A yau Jumma'a 7 ga wata ne Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing cewa, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin da ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Ghana suna mai da hankali kan yadda lamari yake gudana, suna kuma himmantuwa wajen ba da kariya da taimako ga Sinawan da ke Ghana, a kokarin tabbatar da tsaron lafiya da halaltattun hakkokinsu.
Hong Lei ya kara da cewa, tuni ma'aikatan ofishin jakadancin kasar Sin da ke Ghana suka ziyarci Sinawan da aka tsare su, tare da ba su abinci da sauran kayayyakin masarufi, sa'an nan suka taimaka musu wajen samun jinya. Har wa yau kuma, wasu ma'aikatan ofishin sun je wuraren hakar zinariyar kasar domin tabbatar da wasu batutuwa.(Tasallah)