Hong Lei ya kara da cewa, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sake tunatar da Sinawan da ke kasar Ghana da su bi dokokin wurin a tsanake, kada su saba wa dokokin kasar. Kuma ma'aikatar da ofishin jakadancin kasar Sin da ke Ghana za su ci gaba da ba da kariya da taimako ga Sinawan da ke kasar, a kokarin tabbatar da tsaron lafiyarsu da halaltattun hakkokinsu.(Tasallah)