in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta cimma nasarar hade kumbunan Shenzhou-9 da Tiangong-1 da hannu
2012-06-24 16:54:48 cri

Yan sama jannatin kasar Sin uku dake cikin kumbon Shenzhou-9 sun cimma nasara a ranar Lahadi da rana gudanar da hadewar farko da hannu tsakanin kumbon Shenzhou-9 da kumbon bincike na Tiangong-1 dake kewayen duniyarmu.

Wannan cimma nasara tana nuna kwarewar kasar Sin kan fasahar zamani na zuwa sararin samaniya da kuma hade kumbuna, haka kuma yana shaida cewa kasar Sin tana iyar tura mutane da jigilar kayayyaki zuwa sararin samaniya.

Dan sama jannati Lui Wang, tare da taimakon abokan aikinsa Jing Haipeng da Lui Yang ya binciki Shenzhou-9 domin hade shi da Tiangong-1 da misalin karfe 12 da mintoci 42. An kara sake hade Shenzhou-9 da Tiangong-1.

Awa guda da rabi, kafin wannan hadewa, kumbon Shenzhou-9 ya rabu da Tiangong-1 kana ya tsaya kusan mita 400 da Tiangong-1.

Bisa nufin bada damar game da kumbunan, kwararru sun kafa domin kumbon tashoshi hudu bisa hanyarsa ta kewayen duniyarmu guda zuwa kilomita 5, mita 400, mita 140 da kuma mita 30 daga Tiangong-1.

An harba Shenzhou-9 zuwa sararin samanaiya a ranar 16 ga watan Yuni daga cibiyar haba kumbuna dake cikin hamadar Gobi a arewa maso yammacin kasar Sin. Kuma an hade da shi da Tiangong-1 a ranar 18 ga watan Yuni.

Hadewa da hannu aiki ne mai wuyar gaske, kuma tana bukatar 'yan sama jannati su yi wannan aiki da hannu a yayin da kumbuna suke kan hanyarsu ta shawaga cikin sararin sama a cikin kilomita 7,8 a kowane kika.

Yan sama jannatin dake cikin Shenzhou-9 zasu komawa cikin Tiangong-1 a cikin 'yan sa'o'i bayan aikin hadewa da hannu kafin su cigaba da aikin gwaje gwaje da binciken sararin samaniya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China