Wu Ping ta fadi haka ne a gun wani taron manema labaru da ofishin watsa labaru na gwamnatin kasar Sin ya shirya yau da yamma.
Bugu da kari, madam Wu Ping ta jaddada cewa, sararin samaniya arziki ne na dan Adam gaba daya, bincike da kuma yin amfani da sararin samaniya buri ne da dan Adam ke neman cimmawa ba tare da kasala ba. kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da yin mu'amala da sauran kasashen duniya bisa ka'idojin girmamawa juna, zaman daidai wa daida da moriyar juna kan yadda za su iya bayar da gudummawarsu tare wajen ciyar da harkokin bincike da nazarin harkokin sararin samaniya gaba da kuma kawo alheri ga jama'ar duk duniya baki daya. (Sanusi Chen)