A ran 31 ga wata, kakakin ofishin watsa labarai na aikin zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya sanar da kudurin da aka yanke a gun taro na 5 na ofishin ba da umurni ga aikin haduwar tauraron dan Adam kirar "Tiangong-1" da kumbo mai lamba Shenzhou-8 cewa, za a harba kumbo mai lamba Shenzhou-8 a ran 1 ga watan Nuwamba da karfe 5 da minti 58 na safe.Don haka a Yau ranar 31 ga watan Oktoba, ne za a sanya makamashi a cikin kumbon.
A halin yanzu, ana gudanar da shirye shiryen harbar kumbo yadda ya kamata.
Kumbo mai lamba Shenzhou-8 kumbo ne da aka kyautata shi sosai, bayan da aka harba shi zuwa sararin samaniya, zai hadu da tauraron dan Adam kirar Tiangong 1 da kansa, ta haka kasar Sin za ta gudanar da aikin haduwar kumbuna masu dauke da mutane a sararin samaniya a karo na farko.(Lami)