in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bukaci Ghana da ta tabbatar da tsaron lafiya da halaltattun hakkokin Sinawan dake kasar
2013-06-05 21:06:16 cri
Ranar 5 ga wata, Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana bayan taron manema labarun da aka saba shiryawa a nan Beijing cewa, kasar Sin ta bukaci kasar Ghana da ta tabbatar da tsaron lafiya da halaltattun hakkokin Sinawan da aka kama, ana kuma tuhumarsu da laifin hakar ma'adinai ba bisa doka ba.

A yayin da yake amsa tambayoyin manema labaru dangane da lamarin, Hong Lei ya ce, tun daga watan Oktoba na shekarar 2012 da ta wuce har zuwa yanzu, gwamnatin kasar Ghana ta dauki jerin matakan yaki da hakar ma'adinai da 'yan kasashen waje suka yi a kasar ba bisa doka ba, ciki har da wasu Sinawa. Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin da ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Ghana sun sa muhimmanci kan lamarin, sun kuma bukaci gwamnatin Ghana da ta kiyaye tsaron lafiyar Sinawan da ke kasar da kuma halaltattun hakkokinsu. Kana kuma ta hanyoyi daban daban ofishin jakadancin kasar Sin da ke Ghana ya sha sanar da 'yan kasar Sin da ke kasar abubuwan da abin ya shafa, tare da tunatar da su da bin dokokin kasar Ghana, da gudanar da ayyuka bisa dokoki, a kokarin tabbatar da tsaron lafiyarsu da halaltattun hakkokinsu.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China