A cikin wani sakon wayar salula da ya aikawa Xinhua, Lazarus ya tabbatar cewa, jami'an tsaro sun mamaye garin Gashua da ke karamar hukumar Bade a arewacin jihar, bayan da wasu masu dauke da makamai suka kaiwa sojojin hari.
A ciki sakon, ya shaidawa Xinhua cewa, "yanzu haka ana ci gaba da fafatawa tsakanin rundunar JTF a jihar Yobe da wasu da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne da suka kaiwa sojojin hari da kuma ofishin 'yan sanda da ke garin Gashua. Kana ya ce daga bisani za a bayar da karin bayani kan lamarin."
Koda ya ke babu wanda ya jikkata a harin, amma mazauna yankin da suka bugawa jami'an tsaro waya, sun shaidawa Xinhua cewa, tun da tsakar dare aka fara musayar wutar tsakanin 'yan bindigar da kuma sojoji. (Ibrahim)