A gasar share fagen shiga wasan na "World Cup" da aka yi a karshen makon da ya gabata, kungiyar kasar Argentina ta doke ta kasar Venezuela da ci uku da nema. Inda Messi ya ciwa kungiyar tasu kwallon guda daya da aka sanya a zare. Bisa hakan yawan kwallayen da ya ciwa kungiyar kasar ta Argentina suka kai 32, wato kwallaye biyu ke nan suka rage masa, ya yi daidai da kwallayen da Maradona ya sanya a zare.
A tarihin kungiyar kasar ta Argentina dai, Gabriel Omar Batistuta ya ciwa kungiyar kwallaye 56, wanda kuma shine ke a matsayi na farko, a jerin 'yan wasan kungiyar mafiya cin kwallo, sai Hernan Jorge Crespo, a matsayi na biyu da kwallaye 36, sannan Diergo Maradona dake matsayi na uku da kwallaye 34.(Zainab)