in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Parkour: wani wasan ne dake bukatar jaruntaka da fasaha
2013-04-20 15:50:56 cri

Yanzu a biranen kasashe daban daban, musamman ma wasu daga manyan birane, a kan ga wasu matasa na guje-guje da sauri a kan titi, suna kuma tsallake shingayen dake gabansu cikin sauki, haka kuma za a ga suna hawa wasu bangwaye masu tsayi sosai, ko kuma su yi tsalle daga saman wani gini zuwa wani, su fado kasa ba tare da ji wa kansu rauni ba. Wannan gudu da tallake wurare da ake yi ya kan ba mutane mamaki, har ma tsoro a wasu lokuta, amma hakika dai wadannan matasa suna wani wasa ne da ake kira Parkour, ko kuma Free-running a Turanci.

Wasan na Parkour wani sabon salon wasa ne da aka fara yinsa a kasar Faransa a shekarun 1980, don haka aka nada masa wannan suna na Faransanci. Ma'anar kalmar ita ce 'gudu a wurare daban daban'. Kamar yadda kalmar ta nuna, masu shiga wasan su kan mai da birni ya zama wani babban fili horoswa, inda za su mai da bangwaye, da matakalar bene su zama shingayen da ake tsallakewa, kana sukan yi kokarin hawa har ma gini mai benaye 4 zuwa 5, domin su kai samansa, daga baya su yi tsalle zuwa saman wani ginin na daban.

Wani dan Faransa ne mai suna David Belle, ya kirkiro wasan Parkour, da nufin karfafa kwarewar mutum, ta fuskar tinkarar wata matsalar da ta abku ba zato ba tsammani, ta hanyar motsa jiki, inda burin da aka sanya ya yi kama da ma'anar wasan Gongfu na kasar Sin. Sai dai Gongfu na sa mutane su koyi fasahar fada, yayinda Parcour ke sanyawa a koyi fasahar tsira. A wasu fina-finan da aka dauka, a kan nuna yadda wani jarumi ya yi amfani da fasahar Parcour domin tsira daga hannun miyagun mutane.

Sai dai tsiran da ake yi a nan tana tare da jaruntaka, da karfin jiki, da fasaha. Wasu suna kallon wasan Parcour a matsayin wata fasahar da ta yi kama da rawa da zane da dai sauransu, ganin motsin da ake nunawa yayin da ake wasan, yana da ban mamaki da kyan gani. Amma matasan da ke rungumar wannan wasa sun fi son mai da shi wata hanyar motsa jiki da karfafa hali. Kasancewar wasan na bukatar mutane su shawo kan tsoro, da kara samun fasahohin tinkarar matsaloli bisa kokarin gudanar da horo.

Wasan Parcour, saboda wuyar fasaharsa, na bukatar a yi shiri sosai kafin a yi shi. Da farko, za a bukaci a samu jan hali, da kwarewa wajen sarrafa jiki, da kara karfin jijiyoyin hannaye, da kafafu, da baya, da ciki. Sa'an nan ana bukatar samun horo da yawa a daki na musamman inda ake samun kayayyakin horaswa kamarsu horizontal bar, da cushion, da dai sauransu, kafin a gwada fasaha a kan tituna.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China