Tawagar hukumar IOC ta bar birnin na Istanbul a daren ranar 23 ga wata, bayan da ta kammala bincike a Tokyo da Madrid. Shugaban kasar Turkiya Abdullah Gul, ya halarci taron bayyana halin da birnin na Istanbul ke ciki, don gane da daukar nauyin shirya wasannin na Olympics, tare da jami'an hukumar kula da harkokin wasannin Olympics na kasar Turkiyan, inda suka nemi goyon baya daga tawagar hukumar ta IOC. Shugaba Gul ya bayyana cewa, idan aka cimma nasarar gudanar da wasannin a birnin Istanbul, hakan zai zama karo na farko na gudanar wasannin na Olympics a nahiyoyi biyu.
Wannan ne karo na biyar da birnin Istanbul ya yi kokarin neman samun iznin gudanar da wasannin na Olympics, inda a baya har karo hudu ya gaza cimma nasarar hakan. Za a gabatar da sakamakon ne dai na wannan karo, a watan Satumbar dake tafe a kasar Argentina.(Zainab)