Mr Blatter ya bayyanawa 'yan jarida cewa, masu shirya wasan na World Cup na kasar Qatar, ba su gabatar da bukatunsu na canja lokacin yin gasa ba. A cewarsa da zarar sun gabatar da hakan, sauran kasashen dake bukatar samun iznin gudanar da gasar, za su yi nazari kan wannan bukatu, sa'annan a sake jefa kuri'u kan kasar da za ta samu izinin gudanar da gasar.
A baya dai kasar ta Qatar ta yi takarar neman wannan bukata ne da Amurka, da Australia, da Koriya ta kudu da kuma Japan, domin neman samun iznin daukar nauyin gudanarda wasan na "World Cup" dake tafe a shekarar 2022.
Bisa al'ada dai akan gudanar da gasar wasan cin kofin na kwallon kafar duniya ne a lokacin zafi, amma yawan zafi a kasar Qatar a irin wannan lokaci, yakan kai 50℃. Wanda a ganin shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta nahiyar Turai Michel Platini, da sauran masu kula da harkokin wasan, ba za a iya yin wannan gasa ta kwallon kafa a irin wannan yanayi ba, domin illar da zafi mai yawa ka iya yi ga lafiyar 'yan wasa. Don haka, suka bada shawarar gudanar da wasan a lokacin sanyi a kasar ta Qatar. Amma idan aka yi wasan a lokacin sanyi, hakan zai kawo babbar matsala ga gasannin wasan kwallon kafa na kasashen Turai. Kamar dai yadda hukumar shirya gasar Firimiya ta Birtaniya ta amince da wannan ra'ayi.(Zainab)