A karon farko 'yan sama jannati na kasar Sin sun shiga kumbon Tian'gong mai lamba 1 dake tafiya a sararin sama

Da misalin karfe 5 na yammacin yau 18 ga wata, mista Jing Haipeng, dan sama jannatin kasar Sin ya samu nasarar bude kofar dakin gwaji na kumbon Tian'gong mai lamba 1 wato tashar gwaji ta farko da kasar Sin ta kafa a sararin sama, sannan ya shiga kumbon Tian'gong mai lamba 1. A waje daya, mista Liu Wang da madam Liu Yang, sauran 'yan sama jannati biyu su ma sun shiga kumbon Tian'gong mai lamba 1. Wannan ya alamta cewa, wannan shi ne karo na farko da 'yan sama jannati na kasar Sin suka samu nasarar shiga na'urar da ta yi kusan shekara 1 tana tafiya a sararin samaniya.
'Yan sama jannati na kasar Sin sun dauki kumbon Shenzhou mai lamba 9 da aka harba a ran 16 ga wata da maraice. Sa'o'i uku da suka gabata ne, kumbon Shenzhou mai lamba 9 da kumbon Tian'gong mai lamba 1 su da kansu ne suka hadu da juna. Bisa shirin da aka tsara, 'yan sama jannatin za su zauna a cikin na'urar Tian'gong mai lamba 1 na tsawon kimanin kwanaki 6. (Sanusi Chen)