A ranar 16 ga wata da yamma da misalin karfe 6 da minti 37, an harba kumbon Shenzhou-9 mai dauke da 'yan sama jannati. Bisa shirin da aka tsara, kumbon zai shiga hanyarsa a tsawon kwanaki sama da 10. Kuma a cikin wannan kewaye na shi zai hada da kumbon Tiangong-1 har sau biyu. Kuma wannan ne karo na farko da kumbunan suka hade da kansu, daga bisani, kuma 'yan sama jannati za su yi shirin gudanar da harhadasu da hannayensu na kansu a karo na biyu.
Daga bisani, a wannan rana da yamma da misalin karfe 3 da minti 24, 'yan sama jannatin suka bude kofar kumbon Shenzhou-9, domin share fagen shiga kumbon Tiangong-1.
Bisa shirin zirga-zirgar kumbo mai dauke da dan Adam, Sin za ta kammala aikin kafa tashar gwaji a sararin samaniya mai dauke da dan Adam nan da shekarar 2020. Fasahar hadar kumbuna na daya daga cikin manyan fasahohi uku na wannan aiki. Dole sai an samu wannan fasaha kafin a cimma kafa tashar gwaji a sararin samaniya. (Fatima)