Mahukunta a kasar Benin sun tabbatar da aukuwar wani yunkuri na juyin mulki soji, wanda aka shirya dai dai lokacin da shugaban kasar Thomas Boni Yayi, ke dawowa daga wani taro da ya halarta a kasar Equatorial Guinea.
Wata sanarwa da babban mai gabatar da kara na kasar Justin Gbenameto ya sanyawa hannu a jiya Lahadi ta ce, wadanda ake zargi da kitsa wannan lamari, sun yi yunkurin hana shugaba Yayi dawowa gida daga ziyarar aikin ne ranar 22 ga watan da ya gabata, da zummar kafa gwamnatin soji a kasar.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai aka cafke mutane da dama bisa zargin sanya hannu cikin shirin gudanar da wannan juyin mulki, ciki hadda Kanar Pamphile Zomahoun, wani jami'in sojin kasar, da wani 'dan kasuwa mai suna Johannes Dagnon, sa'an nan aka gabatar da su gaban mai gabatar da kara domin amsa tambayoyi, daga bisani kuma aka tisa keyar su zuwa gidan yari dake birnin Cotonou.(Saminu)