Lokacin da yake jawabi a bikin mika kamfanin, mataimakin shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya ba da sanarwar cewa, an baiwa kamfanonin biyu masu zaman kansu iznin gina matatar Lu'u-Lu'u a kasar Ghana, yayin da kamfanin cinikayyar ma'adinan kasar PMMC ya fadada na'urorinsa na kawata Lu'u-Lu'u.
Wannan mataki ya dace da manufar gwamnatin kasar na tabbatar da cewa, kasar ta kara inganta bangaren ma'adinai don kara samun kima a kasuwannin duniya.
Mahama ya ce, an yanke shawarar fadada kamfanin Lu'u-Lu'un kasar ne domin a ba da dama ga sassan masu zaman kansu su shiga a dama dasu a harkar samar da Lu'u-Lu'u, hakan ya kasance manufar gwamnatin kasar na mayar da sassan masu zaman kansu a matsayin ginshikin ci gaban da zai kai ga bunkasa sauran sassan tattalin arzikin kasar.