Mataimakin direktan cibiyar yin cinikayya da kasashen waje, Liu Jianjun ya bayyana cewa, a matsayin taron musayar kayayyakin shige da fice mafi girma na kasar Sin, bikin ya kasance wani dandali mafi kyau na sayen kayayyakin kasar Sin. A cikin 'yan shekarun nan, an dauki matakai da dama don sa kaimi ga masana'antu na kasashen waje shiga kasuwannin kasar Sin. A sa'i daya kuma, ya bayyana cewa, Masar da Sin na taimakon juna sosai, kuma hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya da ke tsakanin kasashen Sin da Masar za ta samu makoma mai haske.
A gun taron, mataimakin shugaban kwamitin kasuwanci na birnin Al-kahira Muhammad Al-Raib ya bayyana cewa, masana'antu na kasashen Sin da Masar suna hadin gwiwar domin moriyar juna sosai, kuma ana fatan karfafa dangantakar sada zumunta daga dukkan fannoni a tsakaninsu, da kara bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki tsakaninsu.
Daga ranar 15 ga watan Afrilu zuwa ranar 5 ga watan Mayu, za a shirya taron musayar kayayyakin shige da fice na kasar Sin karo na 113 a birnin Guangzhou da ke kasar Sin.(Bako)