in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci Kenya da ta hanzarta daidaita jinkirin gyara tashar jiragen ruwa ta Mombasa
2013-06-03 13:56:47 cri

Mataimakin shugaban babban bankin duniya reshen nahiyar Afrika Makhtar Diop a jiya Lahadi ya yi kira ga kasar Kenya da ta yi saurin duba al'amarin cunkuso da kuma jinkirin da ake fuskanta a tashar jiragen ruwa ta Mombasa wadda ke lura da kasashen dake wannan yanki, yana mai gargadin cewa, kasar tana fuskantar asarar dimbin kudin ciniki, idan har ba ta daidaita wannan matsala ba domin a samu hanyar aiwatar da ayyukan da suka shafi sauke kayayyaki da jigilarsu yadda ya kamata.

Mr. Diop ya ce, ya kamata gwamnati ta yi hanzari wajen ganin ta warware wannan matsala a tashar jiragen ruwa idan har kasar na son samun riba, a cikin wata sanarwa da bankin ta fitar sakamakon ganawar da mataimakin shugaban bankin ya yi da kuma mataimakin shugaban kasar Kenyar William Ruto a kasar Japan.

Shi dai wannan tashar jiragen ruwan ita ce ta biyu mafi girma da kuma kayan aiki kamar nasu manyan akwatunan daukan kayan da manyan daurin na kaya bayan na Durban dake kasar Afrika ta Kudu, sannan kuma tashar jiragen ruwa ta Mombasa ita ce kofa da ta hada gabashi da tsakiyar nahiyar Afrika, har ila yau wanda aka fi yawan hada hada. Wannan tashar dai tana kula da kasuwancin Kenya, Uganda, Rwanda, Burundi, gabashin jamhuriyar demokradiya na Kongo, arewacin Tanzaniya, kudancin Sudan da kuma Habasha.

Wannan katafaren tashar jiragen ruwa dake kawo miliyoyin kudin ga kasar idan har aka gyara ta za ta iya zama babbar hanyar kasuwanci kamar birnin Dubai na hadaddiyar daular Larabawa kuma zai ba da kwarin gwiwwa ga 'yan kasa da baki wajen zuba jari, inganta kasuwanci, ba da goyon baya ga wassu ayyuka da za su karfafa darajar tashar. Ganin hada hada daukar manyan tan na kaya daga tashar kawai, a shekara ta 2000 ya tashi daga tan miliyan 9.13 zuwa tan 19.93 a shakara 2012, abin da ya kawo karuwa da tan kashi 7.4 a cikin dari.

A lokacin wannan ganawa, Mr. Diop ya ce, kasashe makwabta yanzu haka sun dogara ne a kan kayan da tashar ke kawowa, don haka ya kamata lallai kasar Kenya ta duba yadda za ta gyara wannan cunkoso, sai dai kuma shi ma bankin duniya ya yi alkawarin ba da nata taimakon don ganin hakan ya samu.

A nashi bayanin, mataimakin shugaban kasar ta Kenya William Ruto ya ce, gwamnati tana sane da wannan matsala ta tashar jiragen ruwan ta Mombasa, yana mai tabbatar da cewa, za'a yi iyakacin kokarin ganin an daidaita wannan matsala.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China