in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 6 sun rasu sakamakon wani hari a arewacin Kenya
2013-04-19 10:24:05 cri

Mahukunta a Kenya sun tabbatar da aukuwar wani hari da ya sabbaba rasuwar mutane a kalla 6, baya ga wasu 10 da suka samu raunuka masu tsanani, yayin wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai a wani otel, dake arewacin kasar a daren ranar Alhamis 18 ga watan nan.

Kwamishinan yankin Garissa Maalim Mohamed ne ya bayyana wa manema labaru cewa, maharan da ba a san ko su waye ba guda hudu, sun kutsa kai cikin otel din mai suna "christened Kwa Chege", wanda aka taba kaiwa hari shekara daya da ta gabata, suka kuma bude wuta kan wadanda ke cin abincin dare, ba tare da kakkautawa ba, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane 6 nan take.

Da yake tabbatar da faruwar wannan danyen aiki ga wakilin kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua ta wayar tarho, Maalim ya ce, mahukuntan kasar sun lashi takobin zakulo, tare da hukunta wadanda suka aiwatar da wannan mummunan aiki, domin su fuskanci hukunci.

Kasar Kenya dake gabashin nahiyar Afirka na shan fama da hare-haren bindigogi da gurneti, wadanda sau da yawa suke zargin kungiyar 'yan ta da kayar baya ta Al-shabaab da aiwatarwa kan jami'an tsaro, da ma fararen hula a lokuta daban daban. Musamman ma a yankunan arewa maso gabashin kasar, dake makwaftaka da kasar Somalia mai fama da rikice-rikice.

Kasar ta Kenya dai na kokawa kan yadda hare-haren kan mai uwa da wabi ke barazana ga harkokin yawon shakatawa da ci gaban masana'antu, wadanda suka zamo jigon habakar tattalin arzikinta, bayan farfadowar da kasar ta yi daga rikicin siyasar da ya auku bayan kammalar babban zaben kasar shekaru biyar da suka gabata, rikicin da a wancan lokaci ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 1,200.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China