Mahukuntan kasar Kenya sun tabbatar da cewa, an taba tsare matashin nan da ya hallaka wani sojin kasar Birtaniya a kasar ta Kenya cikin shekarar 2010, yayin da yake shirin samun horo, da nufin shiga kungiyar nan ta Al-Qaeda reshen kasar Somalia, kamar dai yadda ofishin lura da harkokin wajen Birtaniyan ya tabbatar da aukuwar hakan.
A cewar kakakin gwamnatin kasar Kenyan Muthui Kariuki, an tsare matashin mai suna Michael Adebolajo ne a wani wuri dake kusa da kan iyakar kasar da Somalia, yana dauke da fasfon kasar Birtaniya da wani suna sabanin sunansa na ainihi. Kariuki ya ce, bayan damke matashin, an mika shi ga jami'an kasar Birtaniya dake kasar ta Kenya, kamar dai yadda doka ta tanada.
A makon da ya gabata ne dai Michael Adebolajo ya sassoki jami'in sojin mai suna Lee Rigby da wukake a bainal-jama'a, daf da wata barikin soji da jami'in yake aiki dake birnin na Landan, lamarin da ya sabbaba rasuwarsa nan take.
An dai cafke Adebolaja tare da wani mutum guda a wurin da lamarin ya auku, bayan da 'yan sanda suka harbe su, aka kuma garzaya da su wani asibiti dake birnin na Landan.(Saminu)