in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Kenya ya bayyana sunayen wasu daga ministocinsa
2013-04-24 09:57:16 cri

A ranar Talata, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya ba da sunayen hudu daga cikin 'yan majalisar zartaswa guda 18 da suka kunshi masana da jakadai wadanda a ganinsa zabsu taimake shi ya cika alkawari da ya yi wa jama'ar kasar Kenya.

Yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Nairobi, Kenyatta ya bayyana sunan wata jakada, Amina Mohammed, mataimakiyar magatakardan MDD kuma mataimakiyar babban darektan shirin kiyaye muhalli na MDD a kasar Kenya (UNEP) a matsayin wacce za ta hau mukamin ministar harkokin wajen kasar.

Shugaba har wa yau ya zabo Henry Rotich wanda shi ne shugaba a sashen binciken tattalin arziki a ma'aikatar kudi ta kasar tun watan Maris na shekarar 2006 ya zamo ministan baitulmalin kasar, kana ya zabo wani malamin jami'a Dr. Fred Okengo Matiangi ya zamo ministan fasahar watsa labarai da sadarwa.

Bugu da kari, shugaban kasar na Kenya ya kuma ba da sunan wani gogaggen ma'aikacin banki, James Wainaina Macharia ya zamo ministan kiwon lafiya. Tuni dai aka mika sunayen wadannan mutane ga majalisar dokokin kasar domin a tantance su.

Kenyatta ya ci gaba da cewa, za'a sanar da sunayen sauran 'yan majalisar zartaswan nan gaba inda ya jadadda cewa, babu wani kalubale wajen cike wadannan gurabe, yana so ne kawai ya yi hakan ta wani salo na daban.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China