in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta sanya lada ga wanda ya bayyana maboyar wasu mutane da take nema ruwa a jallo
2013-06-04 10:26:06 cri

Mahukuntan kasar Amurka za su bada lada da yawanta ya kai dala miliyan biyar, ga duk wanda ya ba da bayanin da zai kai ga cafke ko wane daya, daga cikin wasu mutane da ta ayyana a matsayin 'yan ta'adda, wadanda kuma ke jagorantar kungiyoyin 'yan tada-kayar-baya a yammacin nahiyar Afirka.

Mutanen dai sun hada da jagoran kungiyar AQIM Yahya Abu el Hammam, da jagoran bataliyar "Signed-in-Blood" Mokhtar Belmokhtar. Sai kuma wasu mutanen biyu da za a ba da ladan da ya kai dala miliyan uku a kan kowannensu, wato daya daga jagororin kungiyar AQIM mai suna Malik Aboudelkarim, da kuma kakakin kungiyar MUJWA Oumar Ould Hamaha.

Baya ga wadannan mutane, akwai kuma babbar lada da aka kebe ga wanda duk ya tona maboyar jagoran kungiyar Boko Haram Sheik Abubakar Shekau, wanda yawanta ya kai dalar Amurka miliyan bakwai.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China