A ranar Litinin 13 ga wata ne zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Li Baodong, ya bayyana bukatar tallafawa nahiyar Afirka, da hanyoyin karfafa kwarewarta, ta fuskar yaki da ayyukan ta'addanci, ba kuma tare da gindaya wani sharadi na siyasa ga kasashen dake nahiyar ba.
Li Baodong, ya yi wannan tsokaci ne yayin da aka bude mahawara a zauren kwamitin tsaron MDD, mahawarar da ta mai da hankali kan binciko hanyoyin da za a bi, wajen inganta tsaro, da zaman lafiya a nahiyar ta Afirka.
Li, ya kuma jaddada cewa, matsanancin halin rashin tsaro dake addabar wasu sassan nahiyar ta Afirka, tamkar wani mataki ne na kyankyasar 'yan ta'adda, don haka ya bukaci kasashen duniya da su zage dantse wajen tallafawa Afirka, ta fannin dakile ayyukan ta'addancin ba tare da wani bata lokaci ba, a wani mataki na ba da tsaro ga daukacin sassan nahiyar.
Wakilin kasar ta Sin ya kuma nanata manufar kasarsa, don gane da ba da nata tallafi ga nahiyar Afirka a wannan fage, duba da yadda wannan lamari ya taba shafarta kai tsaye.(Saminu)