in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da dandalin tattaunawa na matsayin koli a kan samun ci gaba da kiyaye muhalli da samar da sabuwar kimiyya da fasaha a birnin Beijing
2010-11-18 16:07:09 cri

A ran 18 ga wata a birnin Beijing, an kaddamar da dandalin tattaunawa na matsayin koli a kan samun ci gaba ba tare da gurbatar da wuri ba da kiyaye muhalli da samar da sabuwar kimiyya da fasaha. Takensa shi ne "Tinkarar sauyawar yanayi". A gun bikin bude dandalin tattaunawar, ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin Wan Gang ya furta cewa, gudanar da dandalin tattaunawa a wannan karo na da ma'ana sosai wajen sa kaimi ga samun ci gaba ba tare da gurbatar da wuri ba da kiyaye muhalli.

Wan ya bayyana cewa, sa kaimi ga samun ci gaba ba tare da gurbatar da wuri ba da kiyaye muhalli, ba ma kawai zai sa kaimi ga yin tsimin makamashi da rage fitar da gurbataciyyar iska da tinkarar sauyawar yanayi ba, har ma zai yi amfani da albarkatu yadda ya kamata, a kokarin kara bukatun kasuwanni, da samar da guraben aikin yi, da samun sabbin fannonin karuwar tattalin arziki. A sabili da haka, wannan ne mahada tsakanin kiyaye muhalli da bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma baki daya.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China