in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da bunkasa tattalin atrziki bisa akidar kiyaye muhalli
2010-11-22 20:21:00 cri

Ran 22 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Jiang Yaoping mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin ya nuna cewa, yayin da ake bunkasa tattalin arziki bisa akidar kiyaye muhalli, kasar Sin za ta ci gaba da samar da yanayin da ya dace ga kamfannonin kasashen waje da su zuba jari a kasar Sin, kuma za ta mai da kamfannonin gida da na waje tamkar daya.

Mr. Jiang Yaoping ya bayyana haka ne a taron manema labaru da majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta shirya. Ya ce, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan masana'antu da tattalin arziki bisa akidar kiyaye muhalli, kuma ta bullo da jerin manufofin tattalin arziki da shirin raya masana'antul Tattalin arziki bisa akidar kiyaye muhalli yana da kyakkyawar makoma, kasar Sin za ta gudanar da manufofi da shirye-shirye a bainar jama'a domin gabatar da dama mai adalci ga kamfannoni daban daban, ciki har da kamfannoni masu jarin waje. [Musa Guo]

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China