in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin matasa da wasannin motsa jiki na kasashen Faransanci na taro a Niamey a Nijar
2013-03-08 11:08:01 cri

Babban birnin Nijar, Niamey na karbar bakuncin taron ministocin matasa da wasannin motsa jiki CONFEJES karo na 34 tun ranar Alhamis, tare da halartar sakatare janar kungiyar kasa da kasa ta kasashen dake amfanin da harshen Faransanci wato OIF da kuma wakilan kasashe 43 dake kunshe da wannan kungiya, haka kuma an samu halartar manyan jami'an wasannin motsa jiki da kungiyoyin matasa.

Mahalarta taron za su mai da hankali bisa cigaban da aka samu, manyan batutuwan cigaba da kuma kalubalen dake gaban wannan kungiya, haka kuma da muhimmancin batutuwan da suka shafi matasa da kuma wasannin motsa jiki a cikin kasashen kungiyar. Bayan wannan, taron zai gudanar da zaben sabbin mambobin kungiyar, musammun ma zaben sabon sakatare janar da zai maye gurbin Youssouf Fall wanda ya zo karshen wa'adinsa.

Haka kuma mahalarta taron CONFEJES sun nuna giramama ga sojojin kasar Chadi da suka mutu fagen daga a kasar Mali.

Manufar CONFEJES ita ce ta hada kan kasashe, samar da kudade da kayayyaki gami da karfi bisa hangen yin shawarwari ko da yaushe ba tare da nuna jinkiri ba, ta yadda za'a janyo hankalin matasa domin kasancewa ginshikan gina kasashensu da makomarsu da kansu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China