Katambe ya kara bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun nan, mu'amala da ke tsakanin jam'iyyun kasashen biyu ta kara samun ingantuwa. A wannan karo ne, jam'iyyar da ke mulki a jamhuriyar Nijer ta tura wata tawagar da ke kunshe da mutane 15 da suka fito daga jihohi 8 na kasar, don su samu yin nazari a kasar Sin. Ta hanyar yin nazari kuwa, kasar Nijer tana fatan za ta kara zurfafa hadin gwiwa tsakaninta da kasar Sin a fannoni aikin noma, ilmi, da kiwon dabbobi, da makamashi, da shimfida hanyoyi da sauransu, don taimakawa aikin raya tattalin arziki a kasar.
Kwanan baya, bisa goron gayyata da sashen kula da harkokin tuntubawar jam'iyyun kasashen duniya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya yi, tawagar yin nazari ta jam'iyyar PNDS-tarayya ta jamhuriyar Nijer ta kawo ziyara a nan kasar Sin. (Bako)