Jakada Deng ya nuna cewa, zumucin da ke tsakanin kasar Sin da Afirka na da dogon tarihi, wanda ya wuce shekaru 2000, bugu da kari, ranar 10 ga watan Fabrairu, shekarar 2013, ita ce ranar da Sin da Nijeria suka kulla dangantakar diflomasiyya na tsawon shekaru 42, shi ya sa wannan littafi mai suna Sin da Afirka da Mr. Onunaiju Charles ya rubuta zai zama wata kyauta mai daraja sosai ga wannan ranar, ya kara da cewa, Mr.Onunaiju Charles ya rubuta wannan littafi ne sakamakon kokarin da ya yi wajen yin bincike a fannoni daban daban da kuma nazari mai zurfi, cikin littafin,ya bayyana mu'amalar da aka yi a tarihi da kuma yanzu a tsakanin Sin da Afirka, da kuma zarafi da kalubaken da ake fuskanta wajen dangantakar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, har ma da yanayin ci gaban dangantakar Sin da Afirka. Wannan littafi na da muhimmiyar ma'ana ga ayyukan nazarin dangantakar Sin da Afirka, a sa'i daya kuma, littafin zai taimakawa mutane wajen nazarin dangantakar kasa da kasa.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya nuna yabo sosai ga dangantakar hadin gwiwa da ke tsakanin Sin da nahiyar Afirka, musamman ma tsakanin Sin da Nijeria, sabo da a ganinsa dangantakar diflomasiyya da ke tsakanin Sin da Nijeria na da muhimmiyar ma'ana sosai cikin dangantakar kasa da kasa. Ya kuma nuna cewa, Littafi mai suna "Sin da Afirka" da dan Nijeria Mr. Onunaiju Charles ya rubuta ya dubi ci gaban da aka samu wajen dangantakar da ke tsakanin Sin da Nijeria, haka ma tsakanin Sin da Afirka bisa matsayin kasar Nijeria, wannan zai sa jami'ai da kuma jama'ar kasar Nijeria za su iya fahimta dangantakar Sin da Nijeria daga dukkan fannoni, babu shakka littafin zai ba da babban taimako wajen inganta dangantakar kasashen biyu a nan gaba. (Maryam)