Ma'aikatar harkokin ciniki ta kasar Sin ce dai ta dauki bakuncin wannan biki, wanda aka kaddamar da shi a ranar 23 ga wata, kuma burin gudanar da wannan bikin shi ne gabatar wa mutanen kasar Sin kayayyakin gargajiya na kasashen Afirka, taimakawa kamfanonin kasashen Afirka wajen bude kasuwa a kasar Sin, fadada aikin shigar da kayayyaki daga kasashen Afirka zuwa kasar Sin, da kuma sa kaimi ga bunkasuwar cinikayya a tsakanin Sin da kasashe naAfirka. Bugu da kari, ma'aikatar da ta dauki bakuncin bikin ta samarwa kamfanonin kasashen Afirkan shaguna kyauta, ta kuma bada karin gata gare su a fannonin kwastam da yin jingila.
Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan kudin da aka samu a cinikin dake tsakanin Sin da kasashen Afirka a shekarar 2011 ya kai Dalar Amurka biliyan 166.3, rarar kudin da aka samu a kan cinikin dake tsakanin kasashen Afirka da Sin kuwa ta kai dala biliyan 20.1. (Zainab)