in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babu tushe ko kadan kan batun wai Sin na fitar da magungunan jabu zuwa Afirka
2012-12-27 19:56:40 cri
Game da gargadin da kwararru masana a fannin kiwon lafiya na kasashen duniya suka yi kan cewa, wai magungunan da kasar Sin ta hada na jabu kuma sun kwarara zuwa kasashen Afirka, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a birnin Beijing yau Alhamis 27 ga wata, cewar babu tushe ko kadan kan wannan batu, sannan kuma Sin na son yin kokari tare da Afirka wajen inganta hadin kansu ta fuskar kiwon lafiya don amfana wa jama'ar nahiyar baki daya.

Madam Hua ta kara da cewa, kasar Sin ta taimaka wa Afirka wajen gina asibitoci da cibiyoyin yaki da zazzabin cizon sauro, da tura kungiyoyin jiyya zuwa kasashen Afirka, da samar musu magunguna da kayayyakin jiyya, kana da horar da likitocin wurin.

Haka kuma inji Madam Hua, a ko da yaushe kasar Sin ta kan dora muhimmanci kan ingancin magunguna, da yaki da hadawa tare da saida magungunan jabu. Game da batun fitar da magunguna zuwa ketare, kasar Sin ta kan bi ka'idojin kasa da kasa, da samar da takardun shaida ingancin magunguna bisa bukatar hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, da kuma daukar tsauraran matakai a kan batun da ya shafi magunguna jabu. A waje daya kuma, kasar Sin na fatan ganin 'yan kasuwa na kasashen waje su shigad da kayayyaki daga halaltattun masana'antu.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China