A yayin da yake yin shawarwari da 'yan jaridan kasashen waje, mataimakin shugaban sashen yin cudanya da kasashen waje na kwamitin tsakiya na JKS Ai Ping ya bayyana cewa, a cikin shekaru 90 da aka kafa ta, JKS ta tsaya tsayin daka kan gudanar da harkoki bisa ka'idoji hudu na samun 'yanci da adalci, da girmama juna, da kauracewa sa hannu cikin harkokin gida na kasashen waje, tare da neman samun fahimta da hadin gwiwa da juna, a kokarin yin mu'amala da jam'iyyu daban daban na kasa da kasa. Kawo yanzu dai, JKS ta riga ta kafa dangantaka tsakaninta da sauran jam'iyyu sama da 600 na kasashen waje fiye da 160. Ban da haka, an kafa hanyoyi iri daban daban wajen tsara tsarin yin mu'amala tsakanin manyan jam'iyyu na kasa da kasa, yin shawarwari tsakanin manyan jami'an jam'iyyu, kafa dandalin tattaunawa tsakanin jam'iyyu da dama, kira taron karawa juna sani kan kula da jam'iyyu da kasashe da dai makamantansu.(Fatima)