Cao Baijun ya bayyana cewa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana mai da hankali kan aikin yin cudanya tare da jam'iyyu daban daban na kasashen Afirka, kuma bisa tsarin dandalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka, jam'iyyar ta kafa tsarin yin hadin kai da ke kunshi da matakai iri-iri, kuma ta samu babban sakamako a fannonin warware batun gida da bunkasa jam'iyyar da yaki da cin hanci da bunkasa aikin gona da bunkasa al'ummar kasa da kawar da talauci da sauransu.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, a 'yan shekaru da suka wuce, yawan tawagogin jam'iyyun kasashen Afirka da su kan ziyarci a kasar Sin ya karu sosai, kuma jam'iyyu 110 na kasashe 49 na Afirka sun kafa dangantakar hadin gwiwa tare da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin.(Abubakar)