A ranar Laraba, babban jakadan kasar Sin a MDD ya yi kira ga al'ummar kasa da kasa da su taimakawa kasashen dake tsakiyar Afirka su cimma zaman lafiya da dorewa.
Wakilin din-din-din na kasar Sin a MDD Li Baodong ya yi wannan kira ne yayin zaman ganawar kwamitin sulhu na MDD dangane da halin da ake ciki a yankin tsakiyar Afirka.
Li ya ci gaba da cewa, har yanzu ana ci gaba da fuskantar kalubale na tsaro da zaman lafiya a tsakiyar Afirka, musamman ma idan aka yi la'akari da rikice-rikice a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (CAR), da kuma a gabashin jamhuriyar demokradiyar Congo (DRC).
Ya ce, kasar Sin na fatan ganin muhimman bangarori za su dakatar da dukkan fadace-fadace, su kuma warware batutuwa ta hanyar tattaunawa da yarjejeniya, kana ya bukaci al'ummar kasa da kasa su samar da tallafi ga kasashe da kungiyoyi bisa la'akari da ikon mulki da kasashen yankin suke da su.
Jakadan na kasar Sin ya yi nuni ga muhimmancin kawo karshen barazanar da kungiyar 'yan tawayen 'Lord's Resistance Army' ta LRA ke yi a kasashe guda hudu na wannan yanki, inda a yanzu haka ake kyautata zaton kungiyar ta yada zango a Kafia Kingi ta kasar Sudan.
Bugu da kari, Li ya kuma yi gargadi dangane da wasu barazana na daban kamar 'yan fashin teku a yankin Gulf na Guinea, fataucin makamai da ma sauran laifuffuka da a kan aikata daga wace kasa zuwa wace daban.(Lami)